Bangaren kasa da kasa, ya ratay akan kafofin yada labarai na musulunci da kuma kasashen musulmi da su yi amfani da wannan hanya wajen amfana da koyarwar kur’ani mai tsarki da kuma ilmantar da mutane koyarwarsa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Mahdi Taqavi ya sheda cewa ya ratay akan kafofin yada labarai na musulunci da kuma kasashen musulmi da su yi amfani da wannan hanya wajen amfana da koyarwar kur’ani mai tsarki da kuma ilmantar da mutane koyarwarsa a tsakanin sauran al’ummomi, musamman ma wadanda suke da rashin masaniya kana addinin musulunci.
Malamin ya kara da cewa, idan aka yi la’akari da yadda kasashen yammacin turai suke ta fadi tashin ganin sun yada manufofinsu a kan sauran al’ummomin duniya, za a samu cewa suna yin amfani da dukaknin hanyoyin da suke da su ne na sadarwa, a kan haka su ma musulmi su yi amfani da na su domin isar da manufofin addininsu.
Sayyid Taqavi ya ce ya ratay akan kafofin yada labarai na musulunci da kuma kasashen musulmi da su yi amfani da wannan hanya wajen amfana da koyarwar kur’ani mai tsarki da kuma ilmantar da mutane koyarwarsa a cikin sauran al’immomi.
889141