Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo cewa, wata mai sharhi kn lamurran da suke faruwa yau da kullum daga kasar Bangadash ta bayyana cewa, abin da yake faruwa yanzu haka a kasashen musulmi da na larabawa dai ana ganin abubuwan da suke faruwa na bore wanda ya jefa azzaluman shugabanni daga cikinsu cikin fargaba saboda zalunci da danniyar da suke yi kan al’ummominsu wadanda tura ta kai musu bango kamar dai yadda ake shedawa.
Miliyoyin mutanen kasashen larabawa ne suke gudanar da zanga-zangar kalubalantar shugabanninsu da suke sayar da mutuncinsu ga kasashen yammacin turain a cikin kaskanci, domin ganin an samu sauyi na siyasa a cikin harkokin mulki na wadannan kasashe.
Babbar zanga-zangar lumana da ake shedawa yanzu hak a yankin gabas ta tsakiya ita ce ta mutanen kasar Bahrain da kuma kasar Yemen, duk kuwa da cewa kasashen yammacin turai suke goyon bayan wadannan kasshen kai tsaye.
Abin da yake faruwa yanzu haka a kasashen musulmi da na larabawa dai ana ganin abubuwan da suke faruwa na bore wanda ya jefa azzaluman shugabanni daga cikinsu cikin fargaba saboda zalunci da danniyar da suke yi kan al’ummominsu da jama’arsu. 889062