Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: A karo na sha bakwai za a gudanar da gasar Olompik ta karatun kur'ani mai tsarki da hadisan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.A wajan wannan gasar olompik ta kur'ani da hadisai za a baje littafai da kuma dalibai dari uku da takwas daga kasashe kusan saba'in da shidda za su halarci wannan gasar kasar kuma a ranar sha uku ga watan Oban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da misalign karfe tara na safe zuwa sha daya na safe a cibiyar yada ilimi ta Imam Khomeini a birnin Qum za a fara.
890850