Bangaren kasa da kasa: jami'ar Ikland a Newzland daga shekara mai kamawa zata bude wani fanni na nazarin addinin musulunci gay an jami'ar da za su rika karanta fanning sanin Allah wato Ilahiyat da hakan ke nuni da ci gaban da aka samu a wannan jami'a kuma wannan mataki na da matukar muhimmanci a daidai wannan lokaci da ake son nuna adalci da kusanci a tsakanin mabiya addinai mabanbanta.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa: jami'ar Ikland a Newzland daga shekara mai kamawa zata bude wani fanni na nazarin addinin musulunci gay an jami'ar da za su rika karanta fanning sanin Allah wato Ilahiyat da hakan ke nuni da ci gaban da aka samu a wannan jami'a kuma wannan mataki na da matukar muhimmanci a daidai wannan lokaci da ake son nuna adalci da kusanci a tsakanin mabiya addinai mabanbanta.Ya zuwa yanzu a wannan jami'a ana karanta akidar sanin kiristanci ne amma karuwar bukatar da yan jami'a ke nunawa na sanin musulunci da bude wannan fanni ya tilasta wa mahukumtan jami'a daukan wannan mataki na ware wani fanni a jami'ar kamar yadda Zain Ali shugaban bangaren nazarin addinin musulunci a jami'ar ya bayyana a wata tattaunawa day a yi da manema labarai kan lamarin.
891163