Bangaren kasa da kasa;kungiyoyin musulunci ne a kasar ta Indonosiya suka hadu da fahimtar juna suka sanar da ranar lahadi sha biyar ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shmasiya ta zama ranar babbar salla a kasar.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa: kungiyoyin musulunci ne a kasar ta Indonosiya suka hadu da fahimtar juna suka sanar da ranar lahadi sha biyar ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shmasiya ta zama ranar babbar salla a kasar. Bayan an nakalto daga jaridar Jakarta Ta Clob kungiyyar nahadatul Ulma'a da Muhammadiya sun yi amanna da amince da ranar lahadi mai zuwa ta zama ranar babbar salla a fadin kasar har ila yau za a ci gaba da dudanar da shagulgulan babbar sallar a fadin kasar har zuwa ranar litinin .Kuma sun dauki wannan mataki ne karkashin lissafin da suka yi na ganin wata a kasar .
891066