IQNA

Gasar Karatun Kur'ani Na Kasashe Masu Manufa Ta Bai Daya A Tataristan

12:58 - November 02, 2011
Lambar Labari: 2216415
Bangaren harkokin kur'ani: a karo na takwas za a gudanar da gasar karatun Kur'ani da tilawa a ranekun uku da hudu ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin Kazan fadar mulkin jamhuriyar Tataristan kuma wannan gasar karatun Kur'ani ta shafi kasashen da manufofin suka zamanto na bai daya.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa: a karo na takwas za a gudanar da gasar karatun Kur'ani da tilawa a ranekun uku da hudu ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin Kazan fadar mulkin jamhuriyar Tataristan kuma wannan gasar karatun Kur'ani ta shafi kasashen da manufofin suka zamanto na bai daya.Wannan gasar karatun Kur'ani ta shafi mahardata kur'ani da kuma wadanda suka iya kira'a tare da kiyaye dokoki da tsarin karatun kur'ani har ila yau kuma a wannan gasar wadanda za su halarci wannan gasar dole su kasance daga kasashe masu manufa iri daya da kuma za su sanya kayan galgajiya na iyaye da kakannu.


891281
captcha