IQNA

Gasar Adabi Da Fasaha Daga Babbar Salla Har Gadir

Bangaren al'adu da fasaha; ofishin da ke kula da yada al'adun Jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Filipine ya shirya wata gasa ta Adabi da fasaha da aka bawa sunan daga ranar idin babbar salla har zuwa Gadir.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa: ofishin da ke kula da yada al'adun Jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Filipine ya shirya wata gasa ta Adabi da fasaha da aka bawa sunan daga ranar idin babbar salla har zuwa Gadir.A wannan gasar kowa zai nuna kwarewa da Allah ya huwace masa ta hanyar fasaha da kuma adabi kuma wannan wani salon e na kara kusanci a tsakanin masana fasaha da adabi bugu da kari sai kara kusanci a tsakinin musulmi da sanin muhimmancin babbar salla da idi gadir kuma duk wanda yake son shiga wannan gasar yana iya aike sunansa da bayaninsa kan wannan adireshin: ی NO.16 Santa Potenciana St.Urdaneta Village Makati City Metro Manila manila@icro.ir

890464