IQNA

Tsohon Mai Bada Fatawa Na Kasar Uzbakistan Ya Rasu

13:00 - November 02, 2011
Lambar Labari: 2216427
Bangaren siyasa da zamantakewa: Abdul Rashid Kari Bahram Uf tsohon mai bada fatawa da kula da harkokin da suka shafi musulmi a jamhuriyar Uzbakistan ya rasu.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa: Abdul Rashid Kari Bahram Uf tsohon mai bada fatawa da kula da harkokin da suka shafi musulmi a jamhuriyar Uzbakistan ya rasu . Yana rike da wannan mukami ne daga shekara ta dubu daya da dari tara da tis'in da biyar zuwa shekara ta dubu biyu da shidda kuma yana daga cikin fitattun makaranta kur'ani a Uzbakistan da Asiya ta tsakiya kuma ya yi karatun addinin musulunci a gurin ma'aifinsa Abdul mumun kafin ya shiga makarantar firamirai a shekara ta dubu daya da dari tara da saba'in da biyar zuwa da saba'in da tara a makarantar Mir Arab a garin Bakhara sai kuma muassisar musulunci ta Imam Bahari inda ya ci gaba da karatunsa.Kuma shi ne limamin masallacin juma'a na babban masallacin Dala Sheik a garin Tashkand.

891300


captcha