Bangaren kasa da kasa: a ranar ashirin ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a cibiyar kula da harkokin addini a Hiwastan da ke lardin Takzas na kasar Amerika aka gudanar da bukin tunawa da zagayowar irin wannan rana ta haihuwar imam Ali Alnakiy (AS).
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a ranar ashirin ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a cibiyar kula da harkokin addini a Hiwastan da ke lardin Takzas na kasar Amerika aka gudanar da bukin tunawa da zagayowar irin wannan rana ta haihuwar imam Ali Alnakiy (AS).Tunawa da imami na goma na limaman tsira hadarat Imam Ali Alnakiy (AS) a gudanar da shi a wannan cibiya tare da gabatar da jawabai masu gamsarwa da kuma sallar magariba kuma an bude wannan taro ne tare da sauraren karatun kur'ani mai tsarki da sauran shirye shirye masu gamsarwa kamar waken yabo da kawo takaitaccen tarihin rayuwar Imam Ali Alnakiy (AS).
896766