IQNA

Mahajjatan Indiya Sun Gudanar Da Ayyukan Hajjin Bana Cikin Tsaro

Banagren siyasa da zamantakewa; maniyata hajjin bana daga kasar Indiya sun gudanar da ayyukan hajjin bana cikin cikekken tsaro da kwanciyar hankali.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; maniyata hajjin bana daga kasar Indiya sun gudanar da ayyukan hajjin bana cikin cikekken tsaro da kwanciyar hankali.Abubakar Naleeb shugaban komitin hajjin bana daga kasar Indiya ne ya fitar da bayanin cewa; masu kula da ayyukan zirga-zirgar hajjin bana a kasar indiya sun samara da cikekken tsaro ga mahajjatan bana da hakan ya bas u damar gudanar da ayyukansu na hajji a bana cikin kwanciyar hankali da cikekken tsaro kama daga ayyukan da suka gudanar a birnin Madina har zuwa wadanda suka gudanar a birnin makka. Har ila yau shugaban komitin kula da ayyukan hajji na bana a kasar ta Indiya ya fito fili ya bayyana cewa: tare da godiya ga Allah madaukakin sarki a bana masu kula da aikin hajji a Indiya sun dauki matakai masu gamsarwa ta fuskar tsaro ga mahajjanatn kasar da hakan ya bas u damar kammala ayyukan aikin bana cikin tsaro .

895827