IQNA

Taron Idin Gadir Khum A Seraleyon

Bangaren siyasa da zamantakewa: taron shagulgulan idin Gadir Khum da ofishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran ya shira a bana a kasar Seraleyon tare da hadin guiwar karamar jami'ar musulunci ta Friytawun da kuna hadin guiwar hadin kungiyoyin musulunci na Ja'afariya kuma a ranar talata ashirin da hudu ga watan aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a gudanar .
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; taron shagulgulan idin Gadir Khum da ofishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran ya shira a bana a kasar Seraleyon tare da hadin guiwar karamar jami'ar musulunci ta Friytawun da kuna hadin guiwar hadin kungiyoyin musulunci na Ja'afariya kuma a ranar talata ashirin da hudu ga watan aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a gudanar . A wajan wannan taro za a samu halartar jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran da ke kasar ta Seraleyon da kuma kimanin masana da kwararru dari uku da hamsin da suka kware ta fuskar ilimi da al'addun musulunci da suka fito daga garuruwa daban daban da kauyukan wannan kasar da kuma shugabannin kabilun day an jami'a da shugabannin jaridu da kafafen watsa labarai na kasar.

896765