Bangaren al'adu da fasaha: a karo na biyar sabuwar fitowa ta mujjallar musulmin mabiya mazhabar shi'a a mayanmar ta fiti kuma wannan it ace fitowa ta musamman ta wannan wata na Azar na wannan shekara kuma ana raba wannan mujallar kyauta .
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ne ya watsa rahoton cewa; a karo na biyar sabuwar fitowa ta mujjallar musulmin mabiya mazhabar shi'a a mayanmar ta fiti kuma wannan it ace fitowa ta musamman ta wannan wata na Azar na wannan shekara kuma ana raba wannan mujallar kyauta .Wannan mujjalar a ranar juma'ar da ta gabata ashirin ga watan aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne aka watsa ga musulmin kasar mabukata da kuma ta kumshi bayani da sharhi kan lamuran da suka shafi musulmi da rayuwarsu da zaman takewarsu da kuma akida,hadisai.kiwon lafiya da sauran mahangogi na addinin musulunci har ila yau da amsa wasu lamura da suka shafi bangarori daban daban na musulmin kasar. Wannan mujalla mai shafi talatin da biyar tana maudu'ai dari biyar .
897563