Bangaren siyasa da zamantakewa; ma'aikatar da ke kula da harkokin adddini a kasar Aljeriya ta rufe masallatai tari tara da kuma wasu guraren salla dubu daya a yankuna daban daban na wannan kasa a yan shekarun baya bayan nan karkashin fakewa da sha;anin tsaro da kuma rashin samin izinin gudanar da aikinsu.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ne ya watsa rahoton cewa; ma'aikatar da ke kula da harkokin adddini a kasar Aljeriya ta rufe masallatai tari tara da kuma wasu guraren salla dubu daya a yankuna daban daban na wannan kasa a yan shekarun baya bayan nan karkashin fakewa da sha;anin tsaro da kuma rashin samin izinin gudanar da aikinsu.Uddatu Falahu mai bawa ministan kula da harkokin addini shawara a cikin wani jawabi da ya gabatar ya bayyana cewa; kimanin guraben salla dubu daya ne aka rufe kuma sun dauki wannan mataki ne karkashin hadin guiwa da shugabannin lardunan kuma kamar yadda suka samu rahoton matakin yin hakan ya shafi sha'anin tsaro ya kara da cewa: wasu daga cikin irin wadannan guraren ibada suna gudanar da ayyukansu da tarurruka na dora ayar tamtaba da shakku wasu kuwa ba a kula da sha'anin tsabta da gyara muhalli.
897099