Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar na shirin bude wani sabon shafi na yanar gizo na musulmi da nufin isar da manufofinta na siayasa sakamakon bakin jinin da ta yi a tsakanin kasashen musulmi da na larabawa.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, yanzu haka haramtacciyar kasar na shirin bude wani sabon shafi na yanar gizo na musulmi da nufin isar da manufofinta na siayasa sakamakon bakin jinin da ta yi a tsakanin kasashen musulmi da na larabawa musamman ma a cikin ‘yan lokutanan da take fuskantar barazana sakamakon boren al’ummomin larabawa.
Kamar dai yadda ta saba haramtacciyar kasar Isra’ila ta kan yi amfani da munafukai daga cikin kasashen larabawa wajen cimma dukkanin bakaken manufofinta a cikin kasashen musulmi da na larabawa, to a wannan karon ma tana da niyar yin hakan, inda wasu daga cikin munafukan larabawa suke shirye su taimaka mata domin isa da wannan bakar manufa.
Haramtacciyar kasar na shirin bude wani sabon shafi na yanar gizo na musulmi da nufin isar da manufofinta na siayasa sakamakon bakin jinin da ta yi a tsakanin kasashen musulmi, kuma ta shirin yin hakan ne ta hanayar batar da kamanninta tare da yin shigar burtu.
897556