Bangaren kasa da kasa, kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon ta mayar da martani kan zargin masarautar kasar Bahrain ta yi kan cewa ta kame wasu mutane masu alaka da kungiyar suna shirin kaddamar da wasu hare-hare na ta’addanci a cikin kasar da cewa zargi ne maras tushe balantana makama.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakaltio daga shafin sadrawa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-manar cewa, hizbullah ta kasar Lebanon ta mayar da martani kan zargin masarautar kasar Bahrain ta yi kan cewa ta kame wasu mutane masu alaka da kungiyar suna shirin kaddamar da wasu hare-hare na ta’addanci a cikin kasar da cewa zargi ne maras tushe da ake nufin kawar da hankulan al’ummomin duniya da shi dangane da kisan kiyashin da ‘yan kama karya suke yi kan fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana a kasar Bahrain.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zargi ba zai yi tasiri a cikin abin da al’ummar kasdar suke nema ba na neman hakkokinsu wadanda aka haramta musu, kuma hakan ba wani abu ne sabo ba, saboda haka kungiyar ba ta dauki wannan zargi da muhimmancin da za ta yi ta magana akansa ba, domin kuwa duk mai hankali alkali ne kan hakan.
Kungiyar Hizbullah ta kirayi al’ummar kasar Bahrain da su ci gaba da abin da suke yi domin kuwa suna kan gaskiya, kuma Allah yana tare da gaskiya da kuma masu gaskiya a kowane lokaci, kuma da yardar Allah suna kan hanyar tabbatar da nasara a cikin borensu da suke yi ta hanyar lumana, kuma kada duk wata tsokana daga ‘yan kama karya ta sanya su kauce daga neman hakkokinsu ta hanyar lumana. 899234