IQNA

Kungiyar Kasashen Larabawa Ce Mai Kare ‘Yan Daba Da Masu Tsatsauran ra’ayi

13:38 - November 16, 2011
Lambar Labari: 2223362
Bangaren kasa da kasa, ofishin shugaban majalisar malaman ahlu sunna a yankin kudancin kasar Iraki ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake dora alhakin goyon bayan ‘yan daba da masu tsatsauran ra’ayi a kan kungiyar hadin kan kasashen larabawa.

Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na nun cewa, babban ofishin shugaban majalisar malaman ahlu sunna a yankin kudancin kasar Iraki ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake dora alhakin goyon bayan ‘yan daba da masu tsatsauran ra’ayi a kan kungiyar hadin kan kasashen larabawa saboda irin matakan da suka dauka a baya-bayan nan na rashin adalci da rashin sanin ya akamata a kan abubuwan da suke faruwa a kasar Iraki.
Shugaban ofishin sheikh Khalid Mulla ya ce kungiyar kasashen larabawa tana daukar wasu matakai masu ban mamaki a cikin lamurranta a wannan lokaci, musamman ma kan abin da yake faruwa acikin kasashen larabawa, inda take goyon bayan wasu daga cikin gwamnatoci masu murkushe al’ummominsu da suke neman sauyi ta hanyar lumana, tare da mara baya ga wasu ‘yan ta’adda da suke kawo tashin hankali a cikin kasashensu.
Bayanin ya ci gaba da cewa, ofishin shugaban majalisar malaman ahlu sunna a yankin kudancin kasar Iraki ya fitar da wani bayani da a cikinsa yake dora alhakin goyon bayan ‘yan daba da masu tsatsauran ra’ayi a kan kungiyar hadin kan kasashen larabawa wanda hakan, a cewar bayanin babban abin kunya ne.
Da dama daga cikin al’ummomin ksashen larabawa dai suna nuna matukar mamakinsu kan yadda kungiyar ta kara zama wata babbar madaddala ta wanzar da manufofin Amurka da kasashen turai da yahudawan sahyuniya.
899268




captcha