IQNA

Wasu Kasashe Na Yada Gaba Da Iran Domin Kada A Yi Koyi Da juyinta

11:16 - November 17, 2011
Lambar Labari: 2223696
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin kasashen da suka mika kai ga manufofi na siyasar kasashen yammacin turai daga cikin kasashen yankin suna kokarin ganin sun bata sunan Iran da nufin kawar da mutane daga yin koyi da juyinta.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ya gudanar tare da shugaban bangaren isar da sakon muslunci na cibiyar bunkasa al'adu da ilimin muslunci ya bayyana cewa, wasu daga cikin kasashen da suka mika kai ga manufofi na siyasar kasashen yammacin turai daga cikin kasashen yankin suna kokarin ganin sun bata sunan Iran da nufin kawar da mutane daga juyinta na muslunci, musamman ma bayan da al'ummomin larabawa suka farka.

Dagewar da gidan sarautar Saudiyya ta yi wajen ci gaba da kururuta makircin Amurka na batun kokarin kashe jakadan Saudiyyan a Amurka, ya fuskanci mayar da martani daga cibiyoyin diplomasiyyar kasar Iran. A jiya laraba ce dai ofishin wakilin kasar Saudiyya a MDD ya sanar da cewa zai gabatar da wani kudurin korafi kan Iran ga babban zauren MDD.
A cikin daftarin kudurin dai kasar Saudiyyar ta sake gabatar da wannan wasan kwaikwayon na kokarin kashe jakadar kasar a Amurka wanda aka ce wai da hannun Iran cikinsa. Yayin da ya ke magana kan wannan batu, mai magana da yawun ofishin wakilcin Saudiyyan a Abdul Muhsin Ilyas ya ce a jiya laraba ne za su mika daftarin kudurin ga dukkanin membobin babban zauren sannan kuma a ranar juma'a su bukaci a kada kuri'a kansa.
A yayin da yake mayar da martani kan batun, ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Ali Akbar Salehi ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da yadda kasar Saudiyya ta ke ci gaba da dagewa kan wannan wasan kwaikwayon da kasar Amurka ta shirya sai dai ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mai fada da ayyukan ta'addanci, ta yi maraba da wasu bangarori na wannan daftarin da kasar Saudiyya ta gabatar.
Har ila yau Dakta Salehi ya sake jaddada kokarin Iran na tabbatar da yanayi mai kyau da abokantaka da kasar Saudiyya inda ya ce a irin wannan yanayin bai kamata a ce Saudiyya ta ci gaba da daukan irin wannan mataki don kuwa ci gaba da ka-ce-na-ce tsakanin Iran da Saudiya ba lamari ne da ba zai yi dadi da kyau ga al'ummomin kasashen musulmi ba.
Shi ma a nasa bangaren wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na dindindi a Muhammad Khaza'i, cikin wata wasika da ya aike wa shugaban babban zauren , ya ja kunne dangane da abin da zai biyo bayan gabatar da wannan daftarin kudurin kan wannan tuhuma maras tushe da Amurka ta kirkiro sannan kuma Saudiyya take ci gaba da dagewa kansa. Muhammad Khaza'i ya bayyana wannan mataki a matsayin sabuwar bidi'a mai hatsarin gaske wacce kuma ba za a taba amincewa da ita ba sannan kuma wacce za ta zubar da mutumcin majalisar.
Har ila yau wakilin Iran din ya ce idan dai har za ta ci gaba da ba da muhimmanci ga duk wani kuduri da ba shi da tushe, kamar irin wannan da Amurka da Saudiyyan suka gabatar, to kuwa a nan gaba wannan cibiya ta kasa da kasa za ta zamanto wani waje na gabatar da zarge-zarge marasa tushe maimakon wajen tabbatar da hadin kai da aiki tare tsakanin membobinta.
898755

captcha