IQNA

Manyan Malaman Addini A Masar Ba su Yarda Da Shigar Suhula A Kasar Ba

21:29 - November 17, 2011
Lambar Labari: 2223877
Bangaren kasa da kasa, manyan malaman addinin muslunci akasar sun fito kara sun nuna rashin gamsuwarsu da shigar shugula da wasu kasashen larabawa ke yi cikin harkokinsu na cikin gida.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabe cewa, manyan malaman addinin muslunci akasar sun fito kara sun nuna rashin gamsuwarsu da shigar shugula da wasu kasashen larabawa ke yi cikin harkokinsu na cikin gida musamman ma kasar Saudiyya da Qatar da suke kare manufofin Amurka a cikin kasashen larabawa.

A jiya ne ministan harkokin wajen kasar Syria Walid mu'allim ya gudanar da wani taron manema labarai a birnin Damascus fadar mulkin kasar, taron da ya samu halartar wakilai na kafofin yada labarai na cikin gida da kuma kasashen ketare.
A wannan zaman taro Walid Mu'allim ya bayyana matsayin gwamnatin Syria dangane da matakin da kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta dauka na dakatar da Syria a matsayinta na mamba a kungiyar, inda ya bayyana cewa matakin ya sabawa dukkanin ka'idoji da aka kafa kungiyar a kansu, wanda kuma Syria na kan gaba wajen kafa wannan kungiya.
Ya ce Syria tana da cikakkiyar masaniya dangane da abin da aka shirya na makarkashiya a kanta a zaman taron kungiyar kasashen larabawa, amma duk da haka tana fatan larabawan za su koma cikin hankalinsu, domin aiwatar da abin da yake daidai, domin warware matsalolin da kasar Syria take fama da su, da hakan ya hada da dakatar da bayar da makudan kudade ga kungiyoyin 'yan ta'adda da suke kai hare-hare a kan jami'an tsaro da fararen hular Syria, wanda ya ce wasu daga cikin kasashen larabawan yankin tekun fasha ne ke da alhakin hakan, da kuma dakatar da shigo da makamai zuwa ga 'yan ta'addan daga kasar Turkiya.
899433


captcha