Kamfanin dilalncin labara iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-manar cewa, a cikin wani jawabinsa jakadan kasar Syria a kasar Amurka ya jaddada cewa raba dangantaka tsakanin Iran da kuma kasar Syria ba abu ne mai yiwuwa ba kamar yadda wasu suke mafarkin ganin haka sakamakon makircin da ake kitsa ma kasar a halin yanzu.
Tun bayan da kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta dauki matakin dakatar da Syria daga cikin mambobinta, bisa matsin lambar Amurka da kasashen yammacin turai, masana harkokin siyasar duniya ke ganin cewa hakan some-some ne na daukar matakai na yin amfani da karfin soji kan kasar Syria, domin kuwa wannan shi ne abin da ya faru kan kasar Libya, inda turawan yammacin turai suka yi amfani da kungiyar kasashen larabawa wajen halasta kaddamar da yaki kan al'ummar Libya da sunan kare fararen hula daga hare-haren Gaddafi.
Yayin da wasu daga cikin masanan suke ganin cewa kungiyar kasashen larabawan tana bin salon siyasa ne na harshen damo, domin kuwa ta dauki wannan mataki a kan Syria bisa hujjar cewa Syria ba ta aiwatar da abin da dauki alkawali na kawo karshen ayyukan soji a cikin yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula ba, duk kuwa da cewa kasashen larabawa babu wani katabus da suka yi wajen ganin sun gamsar da 'yan bindigar Syria domin ajiye makamansu, saboda haka matsin lamabarsu ya takaita ne kawai kan gwamnati, wanda kuma hakan a hankalce ba zai iya haifar da mai ido ga duk wani yunkurin zaman lafiya a Syria ba.
A daidai lokacin da kungiyar kasashen larabawa take matsa lamba kan gwamnatin Syria, wadda take yin fito-na fito da mutanen da suke dauke da makamai, amma kuma a lokaci guda kungiyar ta kauda kanta daga dukkanin ayyukan kisan kiyashi da muzgunawa fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana da gwamnatin Bahrain ke yi, maimakon haka ma kasashen da suka shiga gaba wajen tilasta ma sauran larabawa su amince a fitar da Syria daga cikin kungiyar kasashen larabawa, kamar su Saudiyya da Qatar da kuma hadaddiyar daular larabawa, su ne suka aike da dakarunsu zuwa kasar Bahrain domin murkushe zanga-zangar lumana da kashe fararen hula.
Jim kadan bayan sanar da wannan mataki na kungiyar kasashen larabawa a yammacin Asabar din da ta gabata, miliyoyin mutane sun fito a dukkanin biranan kasar Syria suna yin Allawadai da hakan, yayin da wasu suka afka kan ofisoshin jakadancin kasashen Saudiyya da Qatar a birnin Damascus, inda suka zargi wadannan kasashe biyu da zama 'yan koren Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila da sauran kasashen yammacin turai, tare da aiwatar da siyasarsu kan kasashen larabawa, a lokacin da shi kuma ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov ya bayyana cewa Amurka da Faransa su ne manyan munafukan da suke kulla wa Syria makirci ta hanyar kasashen larabawa.
To ko ma dai yaya lamarin yake, daukar nauyin aiwatar da manufin siyasar Amurka da kasashen turai a kan Syria da wasu kasashen larabawa suke yi, ba zai haifar da da mai ido ga makomar siyasar yankin gabas ta tsakiya ba, domin kuwa babbar manufar kasashen yammacin turai ba taimakon al'ummomin larabawa ba ce, babar manufarsu ita ce bayar da kariya ga haramtacciyar kasar Isra'ila, da kuma wawashe arzikin da kasashen larabawan suke da shi.
900148