Bangaren kasa da kasa: karkashin wani bincike da Felice Dassetti malamin jami'ar Katolik Louvain ya gudanar ya bayyana cewa; daya cikin hudu na al'ummar garin Bruksel babban birnin Baljuim musulmi ne.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: karkashin wani bincike da Felice Dassetti malamin jami'ar Katolik Louvain ya gudanar ya bayyana cewa; daya cikin hudu na al'ummar garin Bruksel babban birnin Baljuim musulmi ne.Wannan bincike day a gudanar ya nuna cewa; kimanin musulmi dubu dari biyu da hamsim n eke rayuwa a wannan birnin na Bruksel da wannan adadi ke nuni da cewa kashi daya cikin hudu na al'ummar birnin ne kuma ya kara da cewa musulmin birnin na kara himma matuka wajan yada addinin musulunci a wannan birnin da hakan ke nufin yawan musulmi zai karu musamman idan aka yi la'akari da yadda musulmin ke kara cudanya da takwarorinsu na birnin ta fuskar shirya wasanni da tattauawa na tarorrukan fahimtar juna.
900417