Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a Palsdinu ta yi kashedi kan matakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke son dauka na rusa gadar Babul Magariba mai zuwa Masallacin Aksa.Kungiyar ta shaidawa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da kart a kuskura ta zartar da matakin da take son dauka na rusa wannan kada da ke a matsayin tamkar wani abu dab a ya rabuwa da masallacin Kudus mai tsarki.
900441