Bangaren kasa da kasa, Limaman Juma’a a sassa daban-daban na kasar Lebanon da ma wasu daga cikin kasashen larabawa sun babbaya cewa gwamnatin kasar Syria ba za ta mika kai ga matsin lambar kasashen larabawa ‘yan koren Amurka da yahudawan sahyuniya ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad cewa, da dama daga cikin l Limaman Juma’a a sassa daban-daban na kasar Lebanon da ma wasu daga cikin kasashen larabawa sun babbaya cewa gwamnatin kasar Syria ba za ta mika kai ga matsin lambar kasashen larabawa ‘yan koren Amurka da yahudawan sahyuniya ba, musamman ma na yankin tekun fasha wadanda maitarsu ta fito fili wajen zartar da manufofin turai a cikin kasaashen larabawa da na musulmi.
Yankewa kasar Syri'a wa'adi mataki ne na gaggawa da wannan kungiyar ta dauka wanda ya ke iya zama umarni ne su ke zartarwa na manyan kasashe.
Tsoma bakin na kasashen larabawa a harkokin cikin gidan kasar Syria zai iya dagula lamurra da kuma zurfafar rikicin da kasar ta ke fama da shi.
A cikin watannin bayan nan mutane Syria sun bukaci da a samar da sauye-sauye kuma gwamnatin kasar ta amsa da cewa za ta yi hakan. A cikin wannan yanayin 'yan kore na cikin kasar Syria wadanda su ke da alaka da kasashen waje su ka fara amfani da karfin makami domin haddasa hargitsi acikin kasar. Kama 'yan ta'adda masu yawa da suka fito daga kasashe daban-daban na larabawa a cikin syria yana nuni da yadda su ke son haddasa fitina. Kuma jami'an tsaron kasar Syria sun kama makamai masu yawan gaske daga 'yan ta'addar.
Sai dai wannan bai sa gwamnatin ta Syrai ta rufe kofar samar da sauye-sauyen Siyasa ba da su ka hada da kokarin rubuta sabon kundin tsarin mulki.
900491