Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habart cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyoyin habbaka lamurran zamantakewa a Masar cewa, matar shahid Rasha Ali ta bayyana cewa tun ranakun farko da matasa suka fara bore a cikin kasashen larabawa, an tabbatar da cewa hanyar sadarwa ta yanar gizo ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen isar dasakonnin da ake bukata mutane su sani dangane da boren fadin kasa baki daya.
Matasan Tunisia sun yi amfani da irin wannan hanaya suma, a wani labarin da ya shafi Tunisia kuma an habarta cewa shugaban kungiyar al-Nahdha ta masu kishin musulunci a kasar Tunisiya Rashid al-Ganushi ya ce, a yau litinin ne za a sanar da sakamakon tattaunawa akan kafa sabuwar gwamnati.
A yayin wata ziyarar aiki da ya kai a kasar Aljeriya a jiya lahadi Sheikh Rashid al-Ganushi ya fadawa kamfanin Dillancin Labarun Aljeriya cewa: "A karshen wannan watan na Nowamba ko kuma a farkonsa ne za a kafa sabuwar gwamnati ta farko bayan juyin juya hali."
Shugaban na kungiyar Nahdha ya kara da cewa: " Abu ne mai yiyuwa Hamadi al-jabaly ya zama shugaban kasar na farko a karkashin gwamnatin gamin gambiza da za a kafa."
A ranar talata ne za a yi taron majalisar kasa da za a zabi shugaban kasa sannan kuma a cimma matsaya dangane da dokoki na baidaya da za a yi amfani da su wajen tafiyar da bangarori gwamnati, daga nan kuma sai zabar pira ministan da shugaban kasa zai yi."
897073