IQNA

Mutanen Masar Sun gane Koren Da Suka Yi Dangane Makomar Juyinsu

16:02 - November 23, 2011
Lambar Labari: 2227844
Bangaren kasa da kasa, tsohon kakakin kungiyar yan uwa musulmi a kasar Masar ya fadi jiya a dandalin Tahrir da ke birnin Alkahira cewa mutanen masar sun tafaka babban kure a lokacin da suka bar komai sake bayan kayar da gwamnatin Mubarak.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi ta kasar Masar cewa, Kamar Halbawi tsohon kakakin kungiyar yan uwa musulmi a kasar Masar ya fadi jiya a dandalin Tahrir da ke birnin Alkahira cewa mutanen masar sun tafaka babban kure a lokacin da suka bar komai sake bayan kayar da gwamnatin Mubarak tun afarkon shekarar nan da muke ciki.
A bangare guda kuma an sanar da cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin ceton kasa a kasar Masar yayin zaman taron da ya hada majalisar koli ta sojoji da 'yan siyasa. Wani dan siyasar da ya bayyana bukatar yin takarar shugaban kasa da ya halarci taron Mohamed Selim Al-Awwa, ne ya bayyana ma kamfanin dillalanci labaran Masar Mena hakan.
Ya ci gaba da cewa, an cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa wadda aikinta shine na tabbatar da gurin juyyin juya halin 25 ga watan Janeru, a wannan zaman shawarar da sojojin dake rike da ragamar kasar tun bayan gushewar Hosni Mubarak a watan Fevrier suka kira. Sai dai Mohamed Awwa, bai bada wani cikakken bayyani ba kan zaman taron da aka yi da mataimakin shugaban majalisar sojojin Sami Annan, da jam'iyun siyasa musamman 'yan uwa musulmi.
Wata majiya ta sojoji ta shaida ma AFP cewa, majalisar sojojin ta tabo batun yiyuwar nada tsofon jagoran hukumar makamashin nukiliya AIEA Mohamed Elbaradei, a matsayin framinista don maye gurbin Essam Charaf da yayi murabus jiya.
903065

captcha