IQNA

Babban Sakataren Kungiyar kasashen Musulmi Zai Nufi Kasar Libya

22:39 - November 23, 2011
Lambar Labari: 2227974
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar kasashen musulmi Akmaluddin Auglo na da shirin zuwa kasar Libya domin ganawa da sabbin mahukuntan kasar bayan kawo karshen mulkin kama karya na Mu’ammar Gaddafi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na OCI cewa, babban sakataren kungiyar kasashen musulmi Akmaluddin Auglo na da shirin zuwa kasar Libya domin ganawa da sabbin mahukuntan kasar bayan kawo karshen mulkin kama karya na Mu’ammar Gaddafi a cikin watanni biyu da suka gabata.
Kungiyar kasashen musulmi dai na daga cikin kungiyoyin da ba su taka wata rawa wajen kare al’ummomin musulmi a duniya, bisa zargin da ake na cewa manyan kasashen musulmin da suke jagorancin kungiyar duk suna cikin aljihun manyan kasashen yammacin turai na da na yahudawan sahyuniya.
Ya kara da cewa sakataren kungiyar kasashen musulmi Akmaluddin Auglo na da shirin zuwa kasar Libya domin ganawa da sabbin mahukuntan kasar bayan kawo karshen mulkin kama karya na Mu’ammar Gaddafi wanda ya kwashe tsawon shekaru arba’in da biyu yana mulkin kasar Libya.
Yunkurin kasashen yammacin turai na yaudarar kasashe masu tasowa musamman ma kasashen musulmi da na larabawa ya fara kawo karshe lamarin da ke nuni da cewa siyasar danniya ta kasashe masu girman kai ta nufi faduwa na ba da jimawa ba, domin kuwa kasashen musulmi sun fara ganin alamun hakan a cikin wadannan kasashe. 903246
captcha