IQNA

Tunanawa Da Ranar Yancin Labanon Da Wadanda Suka Sadaukar Da Kai

14:34 - November 24, 2011
Lambar Labari: 2228155
Bangaren kasa da kasa: a jiya ne kungiyar gwagwarmya ta kasar Labanon ta gudanar da wani buki a ranar daya ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya tare da fitar da wata sanarwa da a cikin ta jinjiwa mazan jiya wadanda suka sadaukara da kansu wajan kare kasar da kuma suka samara mata da yanci daga hannun yan mulkin mallakar kasar Faransa da kuma bayani kan juriya da tsayin daka dam azan jiya suka yin a fuskantar yan mulkin mallaka da zaluncinsu.

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a jiya ne kungiyar gwagwarmya ta kasar Labanon ta gudanar da wani buki a ranar daya ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya tare da fitar da wata sanarwa da a cikin ta jinjiwa mazan jiya wadanda suka sadaukara da kansu wajan kare kasar da kuma suka samara mata da yanci daga hannun yan mulkin mallakar kasar Faransa da kuma bayani kan juriya da tsayin daka dam azan jiya suka yin a fuskantar yan mulkin mallaka da zaluncinsu. A shekara ta dubu daya da dari tara da arba'in da shidda miladiya ne masu gwagwarmaya da tsayin daka a kasar Labanon suka cimma nasarar fitar da sojojin kasar Faransa daga cikin labanon da hakan ya kai da samin yancin kasar a wannan shekara har la yau a shekara ta dubu biyu da shidda al'ummar Labanon karkashin kungiyar gwagwarmaya ta Hizbulla sun fatattaki sojojin mamaya na haramtacciyar kasar Isra'ila a yakin kwanaki talatin da uku.

903746

captcha