IQNA

Malaman Musulmi A saudiyya Sun Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Rikicin Katif

14:44 - November 26, 2011
Lambar Labari: 2229100
Bangaren kasa da kasa, malaman addinin muslunci na yankin gabacin Saudiyya sun bukaci da a gudanar da bincike kan rikicin da yake faruwa a Katif da kuma kisan kiyashin da jami’an tsaron masarautar kasar suke yi kan fararen hula masuneman sauyi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo cewa, fitattun malaman addinin muslunci na yankin gabacin Saudiyya sun bukaci da a gudanar da bincike kan rikicin da yake faruwa a Katif da kuma kisan kiyashin da jami’an tsaron masarautar kasar suke yi kan fararen hula masuneman sauyi ta hanyar lumana.
A cikin makon nan ne mahukuntan kasar Saudiyya suka bayar da umurni da aharbe duk wanda ya fito yana neman sauyi a cikin harkokin mulkin kasar wanda turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya suka kafa tare da mika shi ga Saud da ‘yan gidansa.
Manyan malaman addinin muslunci na yankin gabacin Saudiyya sun bukaci da a gudanar da bincike kan rikicin da yake faruwa a Katif da kuma kisan kiyashin da jami’an tsaron masarautar kasar suke yi kan fararen hula a cikin wannan mako,wanda hjakan ya yi sanadiyar shadar matasa hudu.
904848

captcha