Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, miliyoyin mutane za su gudanar da zanga-zangar da suka baiwa suna juma’ar shahid a fadin kasar Masar domin nuna rashin amincewa da matakan da mahukuntan sojin kasar suke dauka na neman ci gaba da mulki da wata hanya kamar dai yadda masan ada dama suka fahimci hakan da jimawa.
Kamar dai yadda kungiyoyi, da cibiyoyi daban-daban na ma'aikata da matasa na kasar Masar suka yi kira ga al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatansu don gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a yau juma'a, rahotanni daga kasar sun ce yanzu haka jama'a su yi cikar kwari a dandalin Tahrir Square na birnin Alkahira da kuma wasu manyan birane na kasar inda suke yin kira ga sojojin kasar da su gaggauta mika ragamar mulkin kasar ga fararen hula.
Rahotanni sun ce an samu halartar manyan 'yan siyasa da kuma masu neman sauyi a kasar a zanga-zangar da ake ci gaba da gudanarwa yanzu haka a birnin Alkahira, cikinsu kuwa har da tsohon shugaban hukumar makamashin nukiliyya ta duniya wato Mhd Albarade'i.
Har ila yau wasu rahotannin sun ce wasu mutane sun kai hari a kan bututu mai samar da mai da iskar gaz ga kasashen Jordan da kuma Hki, daga Masar din a tsakiyar ranar yau, harin da kusan shi ne irinsa na 8 da aka kai wa bututun tun daga lokacin da al'ummar kasar suka soma gudanar da tarzomar kin jinin gwamnatin kama karya ta kasar. Shi dai wannan batutu shi ne ke samar da makamashin ga yahudawan Sahyuniya a farashi makaskanci a daidai lokacin da al'ummar kasar ta Masar suke matukar bukatarsa.
904783