Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar sadarwa ta jaridar Intiqad da ake buagawa a kasar Lebanon cewa, an gudanar da wani zaman taro a birnin Beirut na kasar Lebanon kan mahangar Imam Musa Sadr dangane da lamurra da dama da yake yake kallonsu a ailmance da kuma tasirin hakan a cikin rayuwar siyasa da zamantakewar al’umma baki daya.
A bangare guda kuma wanda ya jaoranci sallar Juma'a anan Tehran ya bayyana Amurka a matsayin babbar mai laifi ta daya a duniya wacce ta yi amfani da makamin Nukiliya,Limamin na Tehran ya ci gaba da cewa: Duk da matsin lambar da yammacin turai a karkashin Amurka su ke yi wa Iran dangane da shirinta na makamashin Nukiliya sai dai ba za ta ja da baya ba.
Ayatullah Ahmad Jannati ya ci gaba da cewa: Fitar da kudurori da Amurka da kawayensta su ke yi akan Iran yana nuni ne da rashin sanin alkibla, kuma wajibi ne a gare su su kwana da sanin cewa: Iran ba za ta daina gudanar da shirin nata ba."
Da ya tabo batun zanga-zangar nuna kin jinin tsarin hujja da ake yi a Amurka, limamin na Tehran ya ce: Yadda ake kame da duka da kuma tozarta masu zanga-zangar yana nuni da karyar da gwamnatin Amurka ta ke yi akan kare hakkin bil'adama.
904790