IQNA

Kasar Pakistan Ta Nuna Shirinta Na Yaki Da Ta’addanci A Cikin Watan Muharram

21:30 - November 26, 2011
Lambar Labari: 2229294
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Pakistan ta sha alwashin shiga kafar wando daya da ‘yan ta’adda da suke kaddamar da hare-hare kan masu gudanar da tarukan addini a cikin wannan wata na muharram.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, kasar Pakistan ta sha alwashin shiga kafar wando daya da ‘yan ta’adda da suke kaddamar da hare-hare kan masu gudanar da tarukan addini a cikin wannan wata na muharram a tarukan ashura da mabiya iyalan gidan manzon Allah suke gudanarwa.
A wani rahoton kuma gwamnatin kasar Pakistan ta Allah wadai da hare haren da sojojin NATO suka kaiwa wasu wuraren bincike na jami'an tsaron kasar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar 28 daga cikinsu,Majiyar ma'aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta kara da cewa Priministan kasar ya umurci ma'aikatar ta shigar da korafi kan wadannan hare hare ga kungiyar da kuma gwamnatin Amurka.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Pakistan Tehmina Janjua, ya bayyana cewa jiragen yakin kungiyar sun kai hare hare kan wuraren bincike guda ukku na jami'an tsaron kasar da ke kan iyakarta da kasar Afagnistan inda 28 daga cikinsu suka rasa rayukansu a yayinda wasu 15 suka ji rauni.
Janjua ya kara da cewa gwamnatin kasar zata dakatar da jigilar makamaci wanda kungiyar take amfanin da su a kasar Afganistan don nuna korafinta kan wadannan hareh haren.
904817




captcha