IQNA

Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama Sun Yi Allawadai Da Gidan Sarautar Ali-Saud

15:22 - November 28, 2011
Lambar Labari: 2230712
Bangaren kasa da kasa, mutane 171 dukkaninsu lauyoyi da kuma masu kare hakkokin dan adam a kasar Saudiyya suka yi allawadai da gidan sarautar Ali-saud saboda matakan rashin imani da suke dauka kan fararen hula masu neman sauyi a yankin Katif na gabacin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-tawafuq cewa, mutane dari da sabain da daya dukkaninsu lauyoyi da kuma masu kare hakkokin dan adam a kasar Saudiyya suka yi allawadai da gidan sarautar Ali-saud saboda matakan rashin imani da suke dauka kan fararen hula masu neman sauyi a yankin Katif, musamman a cikin wannan mako da suka kashe akalla fararen hula huda da gangan.

Jami'an tsaro a kasar Saudia sun kara kashe wasu mutane a biyu a yau Asabar a cikin tashe tashen hankula da ke faruwa a yankunan gabacin kasar, shafin yanar gizo ta Bahrain Net ya bayyana cewa, sabon yerima mai jiran gadon na kasar ta Saudia Yerima Naif bin Abdul aziz ya bada umurni ga jami'an tsaron kasar da ke yankin Qadif na gabacin kasar da su kara tsanantawa masu zanga zanga neman sauyi da ke yankin.

Shafin ya kara da cewa jami'an tsaro sun yi dafifi a kan titunan garuruwan yankin sai da ya kai ga a wasu yankuna ba zaka ga wani a kan titi ba, wannan kuwa na faruwa a kan idanun kasashen yammacin turai da suke raya kare hakkin dan adam, da kuma kasashen larabawa masu kakaba takunkumi kan kasar da suka ga dama saboda murkushe masu neman sauyi.
906180

captcha