IQNA

Jam’iyar Masu Kishin Islama A Kasar Morocco Ce Ta Samu Rinjaye A Zaben Kasar

15:21 - November 28, 2011
Lambar Labari: 2230715
Bangaren kasa da kasa, jam’iya masu kishin islama a kasar Morocco ce ta samu babban rinjaye a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar, wanda sama da rabin mutanen da suka cancanci kada kuri’a kasar ba su halarce shi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na iloubnan cewa, jam’iya masu kishin islama a kasar Morocco ce ta samu babban rinjaye a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar, wanda sama da rabin mutanen da suka cancanci kada kuri’a kasar ba su halarce shi, lamarin da ake kallonsa a matsayin zakaran gwajin dafi.
Sakamakon farko na zaben 'yan majalisar kasar Moroko yana nuni da cewa jam'iyyar al-Adala wa al-Tanmiyya mai kishin Musulunci ce take kan gaba da kujeru 80 sannan kuma akwai yiyuwar adadin ya karu sosai a nan gaba.
A wata ganawa da manema labarai da ya yi a jiya asabar don sanar da sakamakon farko na zaben, ministan cikin gidan kasar Morokon Tayyib al-Sharqawi ya ce jam'iyyar Adala wa al-Tanmiyya din ta sami kujeru 80 cikin kujeru 282 da aka tabbatar da sakamakonsu cikin kujeru 395 da majalisar take da su. Ita kuwa jam'iyyar Istiqlal mai mulki a kasar ta sami kujeru 45.
Mahukunta a kasar Morokon sun ce kashi 45 cikin dari na wadanda suka cancanci kada kuri'arsu ne suka shiga cikin zaben, alhali mafi yawa daga cikin al'umma sun kaurace wa zaben bayan da wasu jam'iyyu suka yi kira da a kaurace wa zaben.
An gudanar da wannan zaben ne bayan kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar sakamakon gagarumar zanga-zangar neman sauyi a kasar a farkon shekarar nan lamarin da ya tilasta wa sarki Muhammad na 6 amincewa da sauyi da kuma mika wasu daga cikin ikon da yake da shi ga sabuwar majalisa da kuma firayi minsta.
906012

captcha