IQNA

‘Yan Dabar Masarautar Bahrain Sun Afka Kan masu Gudanar Da Taron Ashura

20:46 - November 28, 2011
Lambar Labari: 2230823
Bangaren kasa da kasa, ‘yan dabar masarautar Bahrain da ake daukowa haya daga kasashen ketare sun afka kan mutanen kasar masu gudanar da tarukan ashura awasu yankunan kasar a ci gaba da murkushe duk wani yunkuri na fararen hula a fadin kasar baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran Iba cewa, bayanai sun tabbatar da cewa yan dabar masarautar Bahrain da ake daukowa haya daga kasashen ketare sun afka kan mutanen kasar masu gudanar da tarukan ashura awasu yankunan kasar a ci gaba da murkushe duk wani yunkuri na fararen hula a fadin kasar, wadda ke da mabiya mazhabar iyalan gidan mazo da dama.
Kasar Bahrain wadda daya ce daga cikin kasashen da suka kada hannu kan a kungiyar hadin kan kasashen larabawa dangane da abin da suka kira yin mafani da karfi kan fararen hula akasar Syria, ita ce kan gaba a cikin kasashen larabawan yankin teken fasha wajen murkushe fararen hula tare da yi musu kisan gilla, saboda sun bukaci sauyi na demokradiyya.
Yanzu haka dai yan dabar masarautar Bahrain da ake daukowa haya daga kasashen ketare sun afka kan mutanen kasar masu gudanar da tarukan ashura awasu yankunan kasar a ci gaba da murkushe duk wani yunkuri na fararen hula a fadin kasar.
905945
captcha