Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo cewa, daya daga cikin malaman addinin muslunci a birnin Qom Sheikh Abduljalil Makrani ya bayyana cewa, mikewar Imam Hussain (AS) domin gwagwarmaya saboda kiyayya da zalunci da tabbatar da martabar addini a bayan kasa ne domin kuwa da ba domin gwagwarmayarsa ba da musulunci na hakika ya zama cikin kwandon tarhi domin kuwa wadanda suke hankoron jan ragamar addini a lokacin sun hannun riga da shi.
Lokacin da Imam Husaini {a.s} ya isa birnin Makkah al'umma sun fito sun tarye shi, kuma mutane suna zuwa masaukinsa dare da rana domin tambayarsa hukunce hukuncen addininsu domin shi ne mafi sanin mutane a zamaninsa kuma jagoran shiriya. Ibnu Kasir a cikin littafin tarihinsa na Bidaya Wan-Nihayah yana cewa: "Mutane sun lizimci zuwa wajen Imam Husaini suna shiga da fita a wajensa, suna zama tare da shi, suna sauraron maganganunsa". Har ila yau Ibnu Kasir ya bayyana dalilin komawar mutane zuwa ga Imam Husaini {a.s} da cewa: Hakika mutane sun koma ga Imam Husaini ne domin shi ne shugaban iyalan gidan Manzon Allallh kuma dan 'yar annabin rahama wanda a wannan lokacin babu wani mutum a bayan kasa da ya fi shi daukaka ko ya yi daidai da shi a matsayi, amma duk da haka daular Yazidu tana hamayya da shi tare da nuna masa kiyayya.
Wasikun Mutanen Kufah Ga Imam Husaini {a.s}. Bayan da mutanen Kufah suka samu labarin halakar Mu'awuya dan Abi-Sufyan da kuma labarin cewa Imam Huasaini {a.s} ya yi hijira zuwa birnin Makkah saboda kin yin mubaya'a ga Yazidu, shugabannin kabilun Kufah sun taru a gidan Sulaiman dan Sarad Al-Khuza'i, inda Sulaiman ke ba su labarin halakar Mu'awuya da kuma matakin da Imam Husaini {a.s} ya dauka na kin yin mubaya'a ga Yazidu da kuma tabbacin cewa Imam Husaini {a.s} ya yi hijira zuwa Makkah, don haka yake ce musu; hakika ku mabiyansa ne kuma mabiyan mahaifinsa, idan har kuna da tabbacin zaku taimaka masa tare da yakar abokan gabansa ta hanyar sadaukar da kai dominsa, to mu dauki matakin rubuta masa sakon wasika kan ya zo gare mu, idan kuma kuna tsoron abin da zai je ya komo da rauni, to kada ku yaudare shi. Sai dukkaninsu suka amsa da cewa; hakika sun amince zasu yaki abokan gabansa tare da sadaukar da kai dominsa, don haka suka rubuta sakon wasika zuwa ga Imam Husaini {a.s} suna gayyatarsa zuwa Kufah, Ibnu Kutaiba a cikin littafin tarihinsa na Imama Was-Siyasa ya nakalto wani abu daga cikin bayanan da sakonnin mutanen Kufah zuwa ga Imam Husaini {a.s} ya kunsa kamar haka.
Godiya ta tabbata ga Allallh da ya kawo karshen makiyinka mai girman kai, azzalumi da ya gudanar da nau'o'in zalunci a kan wannan al'umma, ya danne musu hakkokinsu, ya hana su 'yancin walwala, ya wawushe musu dukiya, kuma ya shugabantar musu da wanda ba su amince da shi ba, sannan ya kashe zababbun wannan al'umma, ya bar mafi sharrinsu, to Allallh ya nisantar da shi daga rahamarsa kamar yadda ya nisantar da Samudawa. Hakika mu a halin yanzu ba mu da shugaba, don haka ka gabato gare mu ko Allah zai sanya mu shiriya da kai.
900599