Bangaren siyasa da zamantakewa: tun ranar bakwai ga wannan wata na azar shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka fara gina masallacin juma'a a garin Sizran da ke lardin Samara na kasar Rasha da kuma matukar aka kammala gina shi da kuma bude shi zai taimaka matuka gaya wajan sauwakewa jama'ar yankin a harkokin ibadodinsu.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ne ya watsa rahoton cewa; tun ranar bakwai ga wannan wata na azar shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka fara gina masallacin juma'a a garin Sizran da ke lardin Samara na kasar Rasha da kuma matukar aka kammala gina shi da kuma bude shi zai taimaka matuka gaya wajan sauwakewa jama'ar yankin a harkokin ibadodinsu.A wajan kaddamar da wannan aiki na fara gina masallacin juma'a a wannan yankin tare da halartar Wa'iz Hadarat Yarullin mai fitar da fatawa a yankin da kuma shuwagabanni da wakilan jama'a a yankin musamman ma wakilan gwamnati da na addini a yankin.
906942