Bangaren kasa da kasa:a karo na sha daya kamar kowace shekara an fara shirin ashura a kasar Bahrain tare da halartar ayatollah Sheikh Isa Kasim shugaban majalisar malammyan shi'ar Bahrain kuma an gaddama a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa' a karo na sha daya kamar kowace shekara an fara shirin ashura a kasar Bahrain tare da halartar ayatollah Sheikh Isa Kasim shugaban majalisar malammyan shi'ar Bahrain kuma an gaddama a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain.Jaridar Alwasat da ke fito wa daga kasar Bahrain ce ta nakalto wannan labari da cewa an kaddamar da wannan shiri ne tare da taken Karbala domin gyara da sulhu .Shi dai wannan shiri na ayyukan al'adu,fasaha da ilimi a fannoni da bangarori daban daban a dabra da jawabai na Huseiniya da tawagar masu juyayin ashura a karkashin gagaramin taron yan shi'a a wannan kasa ta baharain.
907608