IQNA

An Fara Tarukan Azadari na watan Muharram A faransa

Bangaren kasa da kasa: A yau tara ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a dakin gudanar da taro na hadin guiwar kungiyoyi masoya Ahlul Baiti (AS) a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa za a fara gudanar da taron raya ranekun juyayi na shahadar Imam Huseini (AS) da kuma iyalan gidansa da sahabbansa a yankin Karbala.





Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa' A yau tara ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a dakin gudanar da taro na hadin guiwar kungiyoyi masoya Ahlul Baiti (AS) a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa za a fara gudanar da taron raya ranekun juyayi na shahadar Imam Huseini (AS) da kuma iyalan gidansa da sahabbansa a yankin Karbala. Tarurrukan za a fara gudanar da sune a yau da misalign karfe shidda na yamma da kuma za a ci gaba da gudanar da irinsa a wane dare har zuwa goma ga watan Muharrama ranar da Imam Huseini (AS) ya yi shahada a wannan yankin na karbala a zalunci dab a a taba ganin irinsa bad a kuma rashin tausayi da sanin ya kamata inda kafircin makiya addinin Allah ya bayyana a fili a wannan rana da lokaci .Manyan malamai dam asana za su gabatar da bayani da tarihin abubuwan da suka faru a wannan yankin da kuma a wadannan raneku da kuma irin darasin da ke tattare a cikin abubuwa da suka faru a karbala.



907532