IQNA

Yan Shi'a A Keniya Suna tare Da Imam Huseini Da Juyayin Shahadarsa

Bangaren siyasa da zamantakewa; yan shi'a a kasar Keniya a wadannan raneku na juyayin abubuwan da suka faru a watan Muharram na shahadar Aba Abdullah Huseini (AS) ya sahabbasa tare da gudanar da tarukan juyayi da jawabai kan abubuwan da suka faru a wadannan raneku.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa' yan shi'a a kasar Keniya a wadannan raneku na juyayin abubuwan da suka faru a watan Muharram na shahadar Aba Abdullah Huseini (AS) ya sahabbasa tare da gudanar da tarukan juyayi da jawabai kan abubuwan da suka faru a wadannan raneku. A Kowane dare yan shi'a a wannan kasa ta Keniya sun taruwa a cibiyar yan shi'a domin sauraren jawabin malamai da ke bayani kan abubuwa da suka faru na juyayin shahadar imam Huseini (AS) da kuma zaluncin da aka nunawa iyalan igan manzo a yankin karbala tare da la'akari da irin darussan da ke tattare daga lokacin fitowar imam Huseini (AS) da sahabbansa da iyalan gidansa daga Madina zuwa Makka kana daga bisani ya fice zuwa yankin Karbala da kuma abubuwan bakin ciki da suka faru a wannan yanki a rana ta goma ga watan muharram.


906166