IQNA

Mahukuntan Saudiyya Sun Rufe Babbar Husainiyya A Yankin Ihsa Da Ke Gabacin Kasar

21:17 - December 01, 2011
Lambar Labari: 2232534
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Saudiyya bisa umurnin masarautar Ali-Saud da ke bin tafarkin wahabiyanci na gaba da iyalan gidan manzon Allah sun rufe babbar cibiyar gudanar da tarukan addini ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah a yankin Ihsa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar rasid cewa, mahukuntan kasar Saudiyya bisa umurnin masarautar Ali-Saud da ke bin tafarkin wahabiyanci na gaba da iyalan gidan manzon Allah sun rufe babbar cibiyar gudanar da tarukan addini ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah a yankin Ihsa dake gabacin kasar a cikin lardin Katif.
Wannan dai ba shi ne karon faro da mahukuntan kasar Saudiyya suke daukar irin wannan mataki ba na yunkurin murkushe masu neman hakkokinsu a kasar, musamman ma mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah, domin an kame tare da daure dubbai daga cikinsu domin zalunci, kuma masu dasawa da mahukuntan na Saudiyya sun yi shiri da bakunansu.
A cikin wannan makon ne kungiyar kare hakkin bil adama ta amnesty international ta fitar da wani bayani da take tabbatar da cewa, mahukuntan saudiyya suna daddane hakkokin dan adama, tare da kame masu neman sauyi da tsre su babu gaira babu sabar, inda yanzu haka a cewar bayanin akwai dubbai daga cikinsu.
Kasar Saudiyya bisa umurnin masarautar Ali-Saud da ke bin tafarkin wahabiyanci na gaba da iyalan gidan manzon Allah sun rufe babbar cibiyar gudanar da tarukan addini ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah a yankin Ihsa da akasarin mazauna yankin mabiya mazhabar shi’a ne.
908432




captcha