Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad cewa, kungiyar gwagwarmayar musulunci ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakkausar suka tare da yin Allawadai da matakin da kasashen yammacin turai suka dauka na kara kakaba wani takunkumi kan jamhuriyar muslunci ta Iran saboda shirinta na makamashin nukiliya da take aiwatarsa domin amfanin farar hula.
Bayanin ya ci gaba da cewa, a wani labarin kuma da yake da dangantaka da wannan kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Ramin Mehmanparast ya shawarci kasashen Turai da kada su yi wani abin da zai cutar da alakar da suke da ita da Iran sakamakon matsalar da ta kunno kai tsakanin Iran da Birtaniya.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayyana cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a safiyar yau a lokacin da ya ke maraba da jami'an ofishin jakadancin Iran a Ingila da suka dawo gida a safiyar yau bayan rufe ofishin jakadancin Iran din da jami'an Birtaniyan suka yi.
Ramin Mehmanparast ya ce bisa ga dokar da majalisar shawarar Musulunci ta Iran ta kafa, wajibi ne jakadan Birtaniyan a nan Tehran ya bar Iran, to amma a kokarin da jami'an Birtaniyan suke yi na rufe tabarmar kunya da kuma rage kaifin hakan shi ne ya sanya su rufe ofishin jakadancin Iran a can.
Tun dai bayan da Birtaniya ta dau wannan matsayar sakamakon harin da wasu daliban jami'a suka kai wa ofishin jakadancinta da ke nan Tehran don nuna rashin amincewarsu da makircin da Birtaniyan take kulla wa Iran ne ya sanya wasu daga cikin kasashen Turai din yin barazanar rufe na su ofisoshin jakadancin a Tehran, lamarin da jami'an Iran suka ja kunnensu da cewa sakamakon wannan matsaya ta su ba za ta yi musu dadi ba.
909692