IQNA

An Kirayi Musulmin Yankin Kafkaz Da Su Bayar Jini Saboda A Ranar Ashura

19:11 - December 04, 2011
Lambar Labari: 2234250
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar da ke kula da harkokin musulunci a yankin Kafkaz ta kirayi mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke son bayar da jininsu kyauta saboda Allah a ranar Ashura da su kai asbiti domin yin amfani da shi ga masu bukata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na fr.apa cewa, babban mamalin addinin muslunci shekh Allashakur shugaban babbar cibiyar da ke kula da harkokin musulunci a yankin Kafkaz ya kirayi mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke son bayar da jininsu kyauta saboda Allah a ranar Ashura da su kai asbiti domin yin amfani da shi ga masu bukata, tare da yin kira ga dukkanin musulmin yankin da su girmama wannan rana ta bakin ciki, wadda aka cutar da manzon Allah da iyalansa tsarkaka a cikinta.
Malamin ya ci gaba da cewa masu yin juyayi a wannan ranar wajibi ne su san matsayinta da kuma abubuwan da ya kamata akiyaye, domin kuwa yin duk wani abu da ya saba ma muslunci ba zai zama mai amfani ba, kuma Imam Hussain (AS) ba zai jin dadin hakan ba.
Yankin Kafkaz dai na daga cikin yankunan da ake gudanar da tarukan Ashura, bisa la’akari da cewa shi ne yankin da ya fi yawan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a cikin dukkanin yankunan tsohuwar tarayyar Soviet.
Babbar cibiyar da ke kula da harkokin musulunci a yankin Kafkaz ta kirayi mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke son bayar da jininsu kyauta saboda Allah a ranar Ashura da su kai asbiti domin yin amfani da shi ga masu bukata domin yin hakan yana tattare da lada.
909872


captcha