Bangaren kasa da kasa; komitin zartarwa na musulmin kasar Faransa ya fitar da wani bayani da a cikinsa ke yin Allah wadai da daftarin hana sanya kayan musulunci day a hada da sanya Hijabi a guraren shakatawa da kuma guraren renon yara kanana da gwamnatin kasar ke kokarin gabatarwa a gaban majalisar datijawan kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: komitin zartarwa na musulmin kasar Faransa ya fitar da wani bayani da a cikinsa ke yin Allah wadai da daftarin hana sanya kayan musulunci day a hada da sanya Hijabi a guraren shakatawa da kuma guraren renon yara kanana da gwamnatin kasar ke kokarin gabatarwa a gaban majalisar datijawan kasar.Muhammad Musawi shugaban komitin musulmin kasar ta faransa a ranar sha biyar ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne ya fitar da wannan sanarwa da a cikinta yake yin Allah wadai da tofin Allah tsine kan wannan daftari na nuna wariya da banbanci a tsakanin yan kasar ta Faransa.
911414