Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da yaki da tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) yan ta’adda sun kaddamar da harin ta’addanci mafi muni a kan musulmi masu gudanar da tarukan Ashura abirnin Kabul na kasar Afghanistan inda suka yi sanadiyar shahadar mutane sama da sittin tare da jikkata wasu da dama ba tare da hakki ba.
A wani labarin makamancin wannan akalla mutane 16 ne wadanda ke gudanar da juyayin zagayowar ranar Ashura suka yi shahada a sakamakon wani harin bam da aka kai masu a cikin wani masallaci da ke garin Hillah na tsakiyar kasar Iraki a yau litinin.
Rahotanni sun ce baya ga shahadar wadannan mutane 16, akwai kuma wasu mutanen akalla 31 da suka samu raunuka sakamakon wannan hari, wanda har yanzu babu wanda ya fito fili ya dauki alhakin kai shi, to sai dai a cikin lokutan da suka gabata kungiyoyin 'yan ta'adda da ke kare muradun Amurka da kuma gidan Ali Sa'ud na Saudiyya sun sha fitowa fili domin daukar alhakin kai irin wadannan hare-hare a kan masoya Ahlul Baiti a kasar ta Iraki.
Yanzu haka dai a kasashen daban daban na duniya masoya Alhalul Bait Alaihimus salam na ci gaba da gudanar da zaman makoki dangane da zagayowar ranar ta Ashura, wato ranar da dakarun Yazidu dan sarki Mu'awuyyah suka kashe Imam Husein jika Manzon Allah da kuma mabiyansa filin Karbala a shekaru 60 bayan hijrar manzon Allah mai tisra da amincin Allah da iyalensa tsarkaka.
911677