IQNA

Dubun-Dubatar Mabiya Tafarkin Iyalan Gidan Manzo Ne Suka Yi Taron Ashura A Saudiyya

16:59 - December 08, 2011
Lambar Labari: 2235210
Bangaren kasa da kasa, dubban mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ne suka gudanar da tarukan Ashura a yankuna daban daban na kasar Saudiyya, musamman ma ayankunan gabacin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar rasid cewa, dubban mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ne suka gudanar da tarukan Ashura a yankuna daban daban na kasar Saudiyya, musamman ma a yankunan gabacin kasar wadanda akasarin mazaunansu mabiyar mazhabar Ahlul bait (AS) ne.
A daidai lokacin da jamian tsaron kasar Saudiya suke ci gaba da muzguna wa masu zanga zangar lumana ta neman sauyin siyasa a kasar, kungiyar Amnesty International ta fitar da wani rahoto mai shafi 73 dangane da yanayin hakokin dan Adam a kasar. Rahoton wanda a ka buga a shafin yanar gizo na wannan kungiya a jiya 1 ga watan Disamba, ya zargi hukumomin Saudiya da tsare mutane ba tare da gurfanar da su gaban kotu ba, da yanke wa mutanen da ake kamawa hukuncin mai tsawon da ya wuce kima a gidan kaso, da daidaita bayyana adawa da gidan sarautar Al Saudi da aikata taaddanci, da kuma murkushe zanga zangar lumana musamman a yankunan gabashin kasar.
Karuwa da kuma kara karfi da zanga zangar neman sauyi ta ke yi a Saudiya sakamakon motsin da alummomin wasu kasashen Larabawa suke yi da juyin juya hali da yake yaduwa a wannan yanki, ya sa mahukuntan Al Saud suna keta hakkokin bil Adama a fili ba tare da kakkautawa ba. Baya yin watsi da hakkokin yan kasa a fannoni daban daban kamar hakkin fadar albarkacin baki dangane da yanda ake mulkarsu, yanzu kam mahukuntan na Al Saud suna murkushe masu zanga zanga har ma da kashe su ba tare da wani jin dari dari ba.
Gwamnatin Saudiya tana daukar duk wata nuna rashin amincewa da matakan da gidan sarautar Al Saud yake dauka a matsayin laifin taaddanci, kuma duk wanda ya bayyana adawa da Al Saud ya zama dan taadda. Ana yanke wa masu fafutukan samar da sauyin siyasa musu hukunci mai tsanani bayan gudanar da shari'ar jeka-na-yika. A cikin makon da ya gabata jamian tsaron kasar sun kashe masu zanga zanga 6 sun kuma raunata wasu da dama.
A ranar 22 ga watan Nuwamba kotu ta musamman mai hukunta manyan laifuka ta yanke wa mutane 16 wadanda suka hada da fitattun masu fafutukar kawo sauyi su 9 hukuce hukunce daga shekaru 5 har zuwa 30 a gidan yari, a wasu shari'u da ko kadan ba a kiyaye adalci ba wajen gudanar da su, kamar yanda rahoton Amnesty International ya bayyana.
911611

captcha