Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bazmehussain.com cewa an gudanar da tarukan Ashura a birnin Dublin na tsibirin Ireland na kasar Birtaniya tare da halartar mabiya addinin muslunci daga sassa na wannan tsibiri, da suka hada mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da kuma masu bin tafarkin sunna.
A wani labarin kuma yanzu haka ana ci gaba da gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan matsayin Imam Hussain (AS) da kuma gwagwarmayar da ya yi domin daukaka kalmar Allah wanda yanzu haka yake gudana a birnin Lahore wanda kwamitoci guda uku na mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da ke kasar Pakistan suka daukin nauyin shirayaw ada gudanarwa a cikin wannan mako da muke ciki.
Wannan zaman taro yana samun halartar masana daga sassa daban-daban na kasar Pakistan da suka hada da mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da kuma mabiya tafarkin sunna, inda ake gabatar da jawabai nkan matsayin Imam Hussain (AS) da kuma gwagwarmayar da ya yi domin wanzuwar addini muslunci da manzo ya da shi daga Allah.
Yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan matsayin Imam Hussain (AS) da kuma gwagwarmayar da ya yi domin daukaka kalmar Allah wanda yanzu haka yake gudana a birnin Lahore na kaar Pakistan kamar dai yadda aka saba yi. 911474