IQNA

Kungiyar Tarayyar Turai Ta Yi Allah Wadai Da Kona Masallaci A Yammacin Kogin Jodan

16:41 - December 11, 2011
Lambar Labari: 2236836
Bangaren kasa da kasa; Kungiyar tarayyar turai a ranar sha takwas ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da wata sanarwa a a cikinta take yi Allah wadai da harin da yahudawan sahayoniya suka kai wa masallacin Ali Bin Abi Talib (AS) a yankun yahudawa yan share guri zauna tare da cinna masa wuta da cewa bai kamata ba kuma abin Allah tsine cinnawa wani gurin ibada wuta.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa' Kungiyar tarayyar turai a ranar sha takwas ga watan Azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da wata sanarwa a a cikinta take yi Allah wadai da harin da yahudawan sahayoniya suka kai wa masallacin Ali Bin Abi Talib (AS) a yankun yahudawa yan share guri zauna tare da cinna masa wuta da cewa bai kamata ba kuma abin Allah tsine cinnawa wani gurin ibada wuta.Kartin Ishton mai kula da siyasar harkokin waje a kungiyar tarayyar turai ta karanto wannan bayani na yin Allah wadai da cinnawa wannan cibiya kuma masallaci gurin ibada wuta da yahudawan sahayoniya suka yi da cewa: ya zama wani kowa ne mutum ko kungiya sun mutunta hakkokin sauran mutane kuma kar ya yi masu barazana kuma kai wa cibiyar ibadar musulmi hari babu wani dalili da zai kare yinhaka kuma an sabawa doka da hankali.

912459

captcha