Bangaren kasa da kasa:Ikmalul Din Ihsan babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya bayyana cewa lura da kulawa da musulunci na taimakawa wajan kare hakkokin al'umma da mutane da kuma taimakawa mutum a wannan fake da zai say a kara bada himma da kulawa ga addinin Allah day a kumshi kare hakkokin mutane.
Kamfanin dillancin Labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa : Ikmalul Din Ihsan babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya bayyana cewa lura da kulawa da musulunci na taimakawa wajan kare hakkokin al'umma da mutane da kuma taimakawa mutum a wannan fake da zai say a kara bada himma da kulawa ga addinin Allah day a kumshi kare hakkokin mutane. A ranar ashirin ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a daidai lokacin tunawa da ranar duniya ta kare hakkokin bil adama babban sakataren kungiyar hadin kai ta kasashen musulmi ya bayyana cewa: gudanar da ware rana ta musamman wato ranar tara ga watan desamban kowa ce shekara da sunan kare hakkin bil'adam a duniya wata dama ce da dama a gare mu ta sake yin waiwaye da dubi kan karama ta mutum da wajibcin kare wannan karama da Allah ya ba shi kuma babu wani da yafi dacewa da kare masa hakkinsa kamar addinin musulunci.
914033