Bangaren kasa da kasa: taron na birnin Marseil birnin na biyu mafi girma a kasar Faransa da za a gudanar a ranar ashirin da shidda ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya zai maida hankali ne kan fahimtar tsakanin abubuwa guda biyu wato musuluncin Faransawa ko kuma musulunci a kasar faransa ma'ana a tamtamce tsakanin yadda faransawa ke karbar musulunci da kuma yadda musulunci yake a cikin wannan kasa ta Faransa.
Kamfanin dillancin Labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa : taron na birnin Marseil birnin na biyu mafi girma a kasar Faransa da za a gudanar a ranar ashirin da shidda ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya zai maida hankali ne kan fahimtar tsakanin abubuwa guda biyu wato musuluncin Faransawa ko kuma musulunci a kasar faransa ma'ana a tamtamce tsakanin yadda faransawa ke karbar musulunci da kuma yadda musulunci yake a cikin wannan kasa ta Faransa. Da misalign karfe goma na safiyar ranar ce za a bude wannan taron yayin da za a kammala da misalign karfe shidda na yamma agogon birnin na Marseil inda za a samu halartar masana da malamai da kwararru na addini da matrubuta da musulmi a ciki da wajan kasar ta Faransa da za su bayar da bahasi kan wannan take da taron ya kumsa.
914001