IQNA

Taron Tataristan Kan Musulunci Na Adawa da Ta'addanci

Bangaren siyasa da zamantakewa; a ranar ashirin da hudu ga watan Azar shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a cibiyar da ke kula da al'adu na kasa a garin Kazan fadar mulkin kasar Jamhuriyar Tataristan za a fara gudanar da taro mai taken addinin musulunci na adawa da duk wani aiki da ya shafi ta'addanci.

Kamfanin dillancin Labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa : a ranar ashirin da hudu ga watan Azar shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a cibiyar da ke kula da al'adu na kasa a garin Kazan fadar mulkin kasar Jamhuriyar Tataristan za a fara gudanar da taro mai taken addinin musulunci na adawa da duk wani aiki da ya shafi ta'addanci.A wannan taro za a samu halartar masana da jami'ai da malamai da wakilan kungiyoyi da cibiyoyi da hukumomi kamar cibiyar kula da harkokin bada taimako ba na kasuwanci da asusun bada kariya ga harkokin al'adu da ilimi da koyarwar musulunci a kasar Rasha za su halarta domin kowa ya bada bahasi kan yadda addinin musulunci ke adawa da duk wani abu da ya shafi ta'addanci da wuce gona da iri.

914112