Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum Al-sabi ta kasar Masar cewa, a ciki gaba da bayyana ra’ayoyinsu da suke yi kan yunkurin larabawa ‘yan siyasa a Masar ba a bar su a baya ba, domin kuwa Isam Al-iryan mataimakin shugaban jam’iyar adalci da ‘yanci da kungiyar ‘yan uwa musulmi a Masar ya jadda cewa boren da al’ummomin larabawa suke yi na muslunci ne kuma bin ya faru na sakamakon zabe a Masar da Tunisia ya tabbatar da hakan a cewarsa.
Wasu daga cikin masu bin diddigin lamuran da ke kai da komowa suna ganin cewa, duk da hankoron da larabawan suka yi na ganin cewa sun cimma burinsu da manufarsu ta wannan fuska, amma kuma abin takaici kan hakan shi ne yadda kasashen yammacin da karnukan farautarsu daga cikin larabawa suka koma su ne ke jan ragamar juyin larabawa.
Duk wata gwamnati da ba ta dasawa da turawan yamma to ita ce za a kafa ma karan tsana da suna juyi, amma gwamnatocin da suke kare manufofin turawan kuwa, koda suna danne hakkokin al’ummominsu to za a karae kuma a goyi bayansu, ta yadda boren jama’a ba zai iya kayar da su ba.
Isam Al- Iryan mataimakin shugaban jam’iyar adalci da ‘yanci da kungiyar ‘yan uwa musulmi a Masar ya jadda cewa boren da al’ummomin larabawa suke yi na muslunci ne kuma bin ya faru na sakamakon zabe a Masar da Tunisia ya isa ya zama manuniya.
914070